logo

HAUSA

Sin ta bukaci Philippines da ta dakatar da tada zaune tsaye a yankin tekun kudancin Sin

2024-05-17 19:35:34 CMG Hausa

A yau Juma’a ma’aikatar tsaron kasar Sin, ta yi kira ga kasar Philippines da ta kaucewa yin kasada, ta kuma dakatar da duk wasu matakai na keta hakki, da tada zaune tsaye a tekun kudancin Sin.

Da yake bayyana kiran yayin taron manema labarai na rana-rana da ya gudana a yau, kakakin ma’aikatar Zhang Xiaogang, ya ce "Sojojin kasar Sin ba ma fatan ganin tashin wata tarzoma, amma idan fada ya zo, ba za mu ja da baya ba."

Zhang ya kara da cewa, Sin ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da kwararan matakai na kare mulkin kai na yankunanta, da hakkoki da moriyar yankunan teku, da kare zaman lafiya da daidaito a yankin tekun kudancin kasar.

Ya ce, game da batun tekun kudancin Sin, wane ne ke furta wani abu ya kuma aikata sabaninsa? Wane ne yake dagewa wajen tada zaune tsaye, da haifar da tashin tashina? Kuma wane ne ke ingiza yanayin zaman dar-dar da janyo fito-na-fito, da kara lalata yanayin da ake ciki a yankin na tekun kudancin Sin? Ko shakka babu duniya na kallon wadannan abubuwa a zahiri.   (Saminu Alhassan)