logo

HAUSA

Mataimakin shugaban kasar Sin da shugaba Putin sun halarci bikin bude baje kolin hajojin Sin da Rasha karo na 8

2024-05-17 20:38:56 CMG Hausa

A yau Juma’a, mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, sun halarci bikin bude baje kolin hajojin Sin da Rasha karo na 8, wanda ya gudana a birnin Harbin na lardin Heilongjiang, dake arewa maso gabashin kasar Sin.

Yayin bikin kaddamar da baje kolin, Han ya ce, shugaba Xi da shugaba Putin, sun gana a birnin Beijing a jiya Alhamis, sun kuma shata wani sabon mafari, da tsarin bunkasa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa, bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Rasha a sabon zamani.

A nasa jawabin kuwa, shugaba Putin ya ce, Rasha tana martaba kawancen gargajiya tsakaninta da Sin, ya kuma bayyana fatan cewa, sassan biyu za su ci gajiya daga fifikonsu, da yin aiki tare wajen amfana daga baje kolin, don ingiza sabon ci gaban hadin gwiwarsu, a fannoni kamar na raya tattalin arziki, cinikayya, zuba jari, makamashi, masana’antu, da manyan fannonin fasaha da sabbin fasahohi.

Sauran sun hada da hada-hadar sufuri ta kasa da kasa, da yawon bude ido, da noma, da harkokin cikin gida, da nufin samar da karin alherai ga al’ummun sassan biyu.   (Saminu Alhassan)