logo

HAUSA

Yadda Sin da Rasha suke mu’amala da juna ya samar da kwanciyar hankali a duniya

2024-05-17 21:18:22 CMG Hausa

Jiya Alhamis 16 ga wata, an gudanar da bikin kaddamar da shekarar al’adu ta kasashen Sin da Rasha da kuma bikin kide-kide na musamman na murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen 2 a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, lamarin da ya kasance mai matukar muhimmanci a tarihin mu’amalar da ke tsakanin Sin da Rasha. Irin wannan bikin kide-kiden mai kayatarwa, wata alama ce ta dadaden dankon zumunci a tsakanin wadannan manyan kasashen 2.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin da ke ziyarar aiki a kasar Sin, sun yi shawarwari da kuma wani karamin rukunin tattaunawa jiya, inda shugabannin suka takaita kyawawan fasahohin da kasashen 2 suka samu cikin shekaru 75 daga dukkan fannoni, kana sun yi musayar ra’ayoyi dangane da huldar kasashen 2, da manyan al’amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya wadanda suka jawo hankulansu duka, sun kuma tsara sabon kundin raya hadin gwiwar bangarorin 2. Har ila yau, Sin da Rasha sun ba da sanarwar hadin gwiwa da daddale takardun hadin gwiwa da dama, lamarin da ya kara sabon kuzari kan zurfafa huldar kasashen 2.

Yadda Sin da Rasha suke nacewa kan kaucewa kafa kawance da yin fito-na-fito domin wata ta daban, ya nuna fifiko kan yadda aka kafa kawancen aikin soja da siyasa a yakin cacar baki, ya kuma samar da abin misali na sabuwar dangantaka tsakanin kasa da kasa, da kwanciyar hankali a duniya, wadda ke fama da tashin hankali da sauye-sauye.

Ta yaya Sin da Rasha za su samu kyakkyawar makoma? Sun cimma daidaito kan inganta amincewar juna ta fuskar siyasa, kara azamar hadin gwiwa, kara yin koyi da juna ta fuskar al’adu, kyautata tafiyar da harkokin kasa da kasa da dai sauransu.

Sin da Rasha sun samu sakamako da dama cikin shekaru 75 da suka wuce. Nan gaba, wadannan abokan arziki da ke makwabtaka da juna za su ci gaba da hada hannu wajen goyon bayan farfadowar juna, lamarin da zai kara kuzari kan samun wadata da kwanciyar hankali a duniya. (Tasallah Yuan)