logo

HAUSA

Ci gaban huldar Sin da Rasha cikin kwanciyar hankali ya dace da moriyar kasashen biyu

2024-05-16 15:17:13 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum a yau Alhamis. A gun taron, ‘yan jarida sun gabatar da tambayoyi da suka shafi dangantakar Sin da Rasha. Game da hakan, kakakin ma’aikatar Wang Wenbin, ya bayyana cewa, game da dangantakar Sin da Rasha, abin da yake bayyana shi ne, ciyar da huldar Sin da Rasha gaba cikin kwanciyar hankali, hakan ba kawai ya dace da babbar moriyar kasashen biyu da al’ummunsu ba ne, har ma yana da amfani wajen kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da wadatar yankuna, da ma sauran sassan kasa da kasa. (Safiyah Ma)