Putin ya ajiye furannin girmamawa gaban hasumiyar tunawa da ‘yan mazan jiya dake Beijing
2024-05-16 19:50:09 CMG Hausa
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya ajiye furannin girmamawa, gaban hasumiyar tunawa da ‘yan mazan jiya na kasar Sin, wadda ke filin Tian'anmen dake tsakiyar birnin Beijing.
Shugaba Putin ya ajiye furannin ne da yammacin Alhamis din nan 16 ga wata, a ci gaba da ziyarar aiki ta yini biyu da yake gudanarwa a kasar Sin. (Saminu Alhassan)