logo

HAUSA

Sin: Babu Kokwanto Game Da Ikon Sin Na Mallakar Tsibirin Huangyan

2024-05-15 21:05:15 CMG Hausa

A yau Laraba 15 ga watan nan ne dakarun tsaron teku na kasar Sin, suka hango wani jirgin ruwan dakon kaya na dakarun tsaron teku na kasar Philippines, wanda ya yi kutse ba bisa ka’ida ba, daura da tsibirin Huangyan, inda kuma nan take dakarun na Sin suka nemi sanin manufar jirgin ruwan na Philippines.

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce babu tantama game da ikon kasar Sin na mallakar tsibirin Huangyan da ruwan dake kewayensa.

Wang ya ce, a shekarar 2016, kasar Sin ta amince da tsarin kyautatawa, ga wani adadi kadan na jiragen kamun kifi na Philippines, wanda hakan ya ba su damar yin su a sassan ruwan dake kusa da tsibirin na Huangyan.

To sai dai kuma idan har Philippines ba ta martaba kyakkyawan halin kasar Sin don gane da tsibirin ba, Sin din za ta kare hakkokinta na halal, tare da aiwatar da matakan da suka wajaba bisa doka, kamar dai yadda Wang ya bayyana.   (Saminu Alhassan)