logo

HAUSA

Masana za su inganta samun damar amfani da fasahohin zamani ga masu bukata ta musammam a fadin Afrika

2024-05-15 10:19:06 CMG Hausa

Masana sun fara wani taron yini 3 a Nairobin Kenya a jiya Talata, domin inganta samar da damar amfani da na'urori da fasahohin zamani da za su taimakawa mutane masu bukata ta musammam a fadin nahiyar Afrika.

Taron karo na 5 mai taken "Kawar da Shingaye: Inganta Makoma mai Samar da Damar Amfani da  Fasahohi da Na'urorin Zamani ga Masu Bukata ta Musammam a Afrika", ya hada mahalarta sama da 300, da suka hada da masana da masu kirkire-kirkire da 'yan kasuwa da jami'an gwamnati daga fadin nahiyar, domin musayar ilimi kan yadda za a shawo kan abubuwan dake tarnaki ga samun damar amfani da fasahohin zamani ga masu bukata ta musammam.

A jawabinsa na bude taron, manzon musammam na gwamnatin Kenya kan fasahohi, Phillip Thigo ya ce duk da kudurorin taron MDD kan hakkokin masu bukata ta musammam, galibin gwamnatocin Afrika ba sa bayar da cikakken fifikon da ya dace ga samar da damar amfani da na'urori da fasahohin zamani ga masu bukata ta musammam a cikin ajandu ko kasafin kudinsu. (Fa'iza Mustapha)