logo

HAUSA

Kasar Sin ta ba baki masu yawon bude ido dake cikin jiragen ruwa na nishadi izinin shiga kasar ba tare da Visa ba

2024-05-15 14:02:14 CMG Hausa

A yau Laraba, kasar Sin ta zartas ta wata manufa, wadda ta ba baki masu yawon bude ido dake cikin jiragen ruwan nishadi, izinin shiga kasar ba tare da visa ba, a dukkan tashoshin jiragen ruwa da irin wadannan jirage ke shigowa kasar.

Hukumar kula da shige da fice ta kasar Sin ta bayyana cewa, tawagogin masu yawon bude ido kunshe da baki biyu ko fiye dake cikin jiragen ruwa na nishadi, wadanda kamfanonin shirya tafiye-tafiye na kasar Sin suka shirya musu ziyara ko kuma suka shirya karbarsu, za su iya shiga kasar ta tashohin ruwa da irin wadannan jirage ke iya shigar kasar a birane 13 da suka hada da Shanghai da Tianjin da Guangzhou da Sanya da sauransu. (Fa’iza Mustapha)