logo

HAUSA

Antonio Guterres ya bayyana damuwa sakamakon barkewar yaki a El Fasher na jihar arewacin Darfur

2024-05-14 11:19:48 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar damuwa, bisa barkewar tashin hankali a birnin El Fasher, fadar mulkin jihar arewacin Darfur, lamarin da ya jefa sama da fararen hula 800,000 cikin hadari.

Mista Guterres, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, cikin wata sanarwar da mataimakin kakakinsa Farhan Haq ya fitar, ya ce ya kadu da jin rahotannin musayar wuta da manyan makamai a yankuna masu dandazon fararen hula, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dama, da raba wasu da matsugunansu, baya ga lalata ababen more rayuwar jama’a.

Rahotanni dai sun ce a karshen mako, dakarun sojin gwamnatin Sudan na SAF, da na rundunar musamman ta RSF sun yi dauki ba dadi a El Fasher. An ce dakarun RSF sun shafe makwanni suna taruwa a wajen birnin na El Fasher, a wani shiri na kaddamar da hari, yayin da sojojin SAF da mayakan kungiyoyin sa kai na Darfur ke ci gaba da karfafa ikon su a ciki, da kewayen birnin na El Fasher. (Saminu Alhassan)