logo

HAUSA

Kasar Sin: Zargin Samar Da Kayayyaki Fiye Da Kima, Cin Zali Ne

2024-05-14 20:17:30 CMG Hausa

Kasar Sin ta soki zargin da kasar Amurka ke yi mata cewa, tana samar da kayayyaki fiye da kima, inda ta bayyana shi a matsayin cin zali.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ne ya bayyana haka a yau Talata, yayin taron manema labarai da aka saba yi a kullum.

Wang Wenbin ya kara da cewa, Amurka na kare tallafin da take bayarwa, tana bayyana shi a matsayin “jari mai muhimmanci ga masana’antu” yayin da take bayyana makamancin haka daga kasa da kasa a matsayin takara mara adalci.

Ya kara da bayyana munafurcin ra’ayin Amurka, inda take ganin kayayyakin da take fitarwa zuwa ketare a matsayin na “cinikayya cikin ‘yanci” idan suke da fifiko, yayin da take bayyana na wasu kasashe a matsayin wadanda suka wuce kima.

A cewar kakakin, Amurka na amfani da batun samar da kayayyaki fiye da kima domin dakile masana’antun dake samun tagomashi a sauran kasashe, inda take amfani da kariyar cinikayya a matsayin takara mai adalci, lamarin dake take ka’idojin tattalin arzikin kasuwa da ka’idojin cinikayya na kasa da kasa, a wani yanayi dake nuna cin zali karara.

Bugu da kari, Wang ya ce, saurin ci gaban masana’antar sabon makamashi ta kasar Sin ya dace da bukatar duniya ta sauyawa zuwa ga kayayyaki masu kare muhalli, lamarin dake da amfani ga Sin da Amurka da ma duniya baki daya, yana mai cewa, yana fatan Amurka za ta yi watsi da munafurci da kariyar cinikayya da take aiwatarwa. (Fa’iza Mustapha)