Kasar Sin Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Karin Haraji Da Amurka Ta Yi
2024-05-14 20:31:59 CMG Hausa
Kasar Sin ta bayyana matukar rashin gamsuwa da matakin kasar Amurka na kara haraji kan wasu kayayyakin da take fitarwa, ciki har da motoci masu amfani da lantarki da kananan kayayyakin laturoni na Chip da kayayyakin kiwon lafiya.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta fitar a yau Talata. Sanarwar ta kara da cewa, ya kamata Amurka ta gaggauta gyara kuskurenta, ta kuma soke harajin da ta karawa kasar, tana mai cewa, kasar Sin za ta dauki matakan da suka wajaba na kare hakkoki da muradunta. (Fa’iza Mustapha)