logo

HAUSA

An yi kira ga kasashen Afirka da su bunkasa dunkulewa domin habaka fannin yawon bude ido

2024-05-14 10:20:48 CMG Hausa

Ministar ma’aikatar lura da yawon bude ido ta Afirka ta kudu Patricia de Lille, ta yi kira ga kasashen Afirka da su yi aiki tare, wajen bunkasa hade sassan nahiyar ta hanyoyin sufurin sama, da nufin bunkasa yawon bude ido da ci gaban tattalin arziki.

De Lille ta yi kiran ne da yammacin jiya Litinin, yayin taron tattaunawa na ministocin yawon bude ido da ya gudana a birnin Durban na Afirka ta kudu. Ministar ta ce kamfanin (ACSA) ya shirya kashe kudi har kimanin dalar Amurka biliyan 1.18, a aikin bunkasa ababen more rayuwa da ake bukata a filin jirgin saman Afirka ta kudu.

De Lille ta ce "Ragowar sassan duniya na yunkurin saukaka harkokin sufuri, yayin da ake hasashen kara fadadar muhimman kasuwannin fannin na kasashe kamar Sin da India, don haka dole ne mu hada gwiwa wajen saukaka harkokin tafiye tafiye daga tsallake zuwa sassan Afirka, da ma na cikin gidan nahiyar. Yanzu ne lokacin sake nazartar dabarun bunkasa fannin yawon bude ido, da karfafa hade shiyyoyin mu, da yaukaka hadin gwiwa. Dole ne mu karfafa gwiwar hada karfi da karfe tsakanin gwamnatoci da sassa masu zaman kan su bisa matsayin koli, mu ingiza zuba jari a fannin yawon bude ido a shiyyoyi, da sake mayar da hankali ga aiwatar da ayyuka masu tasiri a fannin".  (Saminu Alhassan)