logo

HAUSA

Sin ba ta amince da jita-jitar Birtaniya game da Sinawa masu leken asiri ba

2024-05-14 21:01:58 CMG Hausa

Game da wani labari da aka bayar na cewa, gwamnatin kasar Birtaniya ta kama wasu Sinawa da laifin leken asiri, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin tana lura sosai da wannan batu, kuma ba ta amince da yada jita-jita da Birtaniya ke yi game da zargin wasu Sinawa da leken asiri ba.

An bayar da labarin cewa, gwamnatin Birtaniya ta kama wasu mutane 3 na yankin Hong Kong na kasar Sin, wadanda take zargi da aikata laifin leken asiri.

Wang Wenbin ya bayyanawa ‘yan jarida cewa, a kwanakin baya, Birtaniya ta yi ta yada jita-jitar cewa, Sinawa sun yi mata leken asiri tare da kai hari ta yanar gizo, yana mai cewa, dukkansu zarge-zarge ne marasa tushe, kuma Sin ba ta amince da su ba. Haka kuma, Sin ba ta amince da duk wani yunkurin siyasa ta hanyar amfani da dokoki ko tsaron kasa ba. (Zainab Zhang)