logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci Amurka da ta samar da kyakkyawan yanayin hadin gwiwa kan tinkarar sauyin yanayi da kyautata tsarin raya tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba

2024-05-13 19:33:56 CMG Hausa

Yayin taron manema labarai na yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi bayyani game da batun hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka kan tinkarar sauyin yanayi, yana mai cewa kasar Amurka ta bayyana cewa, tana son yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen tinkarar sauyin yanayi, amma tana zargin kasar Sin da samar da kayayyakin dake amfani da sabbin makamashi fiye da kima. Haka kuma ta ce, za ta kara buga harajin kwastam ga motoci masu amfani da wutar lantarki da kayayyakin da aka samar ta wutar lantarki bisa karfin hasken rana da sauransu da kasar Sin ta kera.

A cewar Wang Wenbin, irin wannan matakin na Amurka ya sabawa ra’ayin da shugabannin Sin da Amurka suka cimma daidaito kan shi a Los Angeles, wato hadin gwiwa don tinkarar sauyin yanayi, kana zai kawo illa ga aikin kyautata tsarin raya tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma kokarin da ake yi wajen tinkarar sauyin yanayi a duniya. Ya ce, Sin na kalubalantar Amurka da ta dakatar da yin abubuwan dake sabawa kudurin da ta tsai da, da samar da kyakkyawan yanayin hadin gwiwa kan tinkarar sauyin yanayi da kyautata tsarin raya tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba.

Game da batun yankin Taiwan kuma, Wang Wenbin ya bayyana cewa, Sin ba ta amince yankin Taiwan ya halarci babban taron kiwon lafiya na duniya ba. Ya ce, wannan kuduri ne na Sin dangane da batun, wanda kuma ya tabbatar da ka’idar “Sin daya tak a duniya”, kana ya tabbatar da kudurin babban taron MDD da babban taron kiwon lafiya na duniya game da wannan batu baki daya. Wang Wenbin ya jaddada cewa, duk wani yunkuri na hana bunkasuwar Sin ta hanyar hura wutar rikici a yankin Taiwan ba zai yi nasara ba, kana kasa da kasa ma ba za su amince da shi ba. (Zainab Zhang)