Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Tabbatar Da Palasdinu A Matsayin Mambar MDD Ba Tare Da Wani Cikas Ba
2024-05-13 20:45:17 CMG Hausa
Kasar Sin ta yi kira ga kasashe masu ruwa da tsaki da kada su kawo cikas ga batun kasancewar Palasdinu mamba a MDD, kuma kada su ci gaba da adawa da kasa da kasa da kokarin tabbatar da adalci a duniya, kana su yi abun da ya kamata.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na yau, lokacin da aka nemi ya yi bayani game da matsayar kasar Sin don gane da batun kasancewar Palasdinu mamba a MDD.
A ranar 10 ga wata ne babban zauren MDD, yayin wani zama na musammam kuma na gaggawa, ya zartas da wani kuduri da gagarumin rinjaye, wanda ya aminci da cancantar Palasdinu ta zama mamba a MDD tare da shawartar Kwamitin Sulhu ya sake nazarin bukatar. Kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka gabatar da kudurin, haka kuma tana cikin wadanda suka kada kuri’ar amincewa.
A cewar Wang Wenbin, suna sa ran ganin Palasdinu ta zama cikakkiyar mamba a majalisar, tare da more cikakkun hakkoki kamar sauran kasashe mambobin majalisar. (Fa’iza Mustapha)