logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Soki Zargin Da Philippines Ta Yi Mata Na Gina Tsibiri A Kusa Da Sashen Tudun Ruwa Na Xianbin Jiao

2024-05-13 20:34:29 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta soki zargin kasar Philippines dake ikirarin kasar ta yi yunkurin gina wani tsibiri a ruwan dake dab da sashen tudun ruwa na Xianbin Jiao, tana mai bayyana shi a matsayin mara tushe.

Manila na ikirarin Beijing ta yi yunkurin gina wani tsibiri a yammacin tekun Philippines ta hanyar lalata wasu duwatsu masu daraja na cikin teku.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin taron manema labarai na kullum, inda ya ce, a baya-bayan nan, kasar Philippines ta yada jita-jita da dama, domin bata sunan kasar Sin da kuma kokarin karkartar da hankalin al’ummun kasa da kasa.

Ya ce, kasar Sin na kira ga Philippines da ta daina maganganun da ba su dace ba, ta fuskanci gaskiya ta kuma koma kan turbar da ta dace wajen daidaita sabanin da ya shafi batun teku dake tsakaninsu, ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.

Xianbin Jiao, sashen tudun ruwa ne dake tekun kudancin kasar Sin da ake kira da Xianbin Reef, wanda Manilla kuma ke kiransa da Escoda. Sashen tudun ruwa na Xianbin Jiao na daga cikin layin tsibiran Nansha Qundao, lamarin da ya sanya shi zama cikin yankin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)