logo

HAUSA

Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin jagororin wasu kamfanonin kasar Sin 2 da saka jari a bangaren haka da kuma sarrafa sinadarin Lithium a jihar Nasarawa

2024-05-12 17:17:28 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ja hankalin masu saka jari ‘yan kasashen waje a bangaren hakar ma’adinai kan su tabbatar suna kiyayewa da hakkin al’umomin yankunan da suke aikin hakar ma’adinan.

Ya bukaci hakan ne ranar Jumma’a 10 ga wata a fadarsa dake birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin shugabannin wasu kamfanonin kasar Sin da suka saka jari a bangaren sarrafa sanadarin Lithium da kuma samar da batura da farantan wutar sola a garin Lafiya dake jihar Nasarawa, ya ce wajibi ne kamfanonin su dauki matakan kare muhallin yankunan da za su gudanar da aikin nasu.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce yana da tabbacin cewa, da zarar ayyukan kamfanin ya kankama, Najeriya za ta kasance babbar cibiyar samar da farantan zuko hasken wutar sola da kuma samar da batura samfurin Ev a nahiyar Afrika baki daya.

“Mun gwada kwazonku a fagen samar da sinadarin batirin Lithium, muna fatan za ku kasance masu gaskiya, kuma na jima ina tunanin cewa me zai hana a rinka samar da irin wadannan batura a nan Najeriya bisa la’akari da irin yanayin da muke da shi, da dimbin matasa masu basira.”

Da yake, shugaban kamfanin Avatar New Energy Materials Mr. Hu Yongwei tabbaci ya bayar na cewa, za su ci gaba da kokarin kyautata yanayin rayuwar al’umomin da suke zaune a yankin da kamfanin yake. “A gaskiya muna son Najeriya, muna son al’ummar Najeriya.”

Shi kuwa shugaban kamfanin Canmax Technologies Mr. Pei Zhenhua wanda ya yi bayaninsa cikin harshen Sinanci ya ce, “Za mu dauki mazauna yankin aiki, inda za su kasance cikin jerin manyan jagororin mulki na kamfanin, sannan wasunsu kuma za su kasance cikin rukunin kwararru a bangaren sarrafa sinadarin da kuma samar da kayayyaki.”

Shi dai wannan sabon kamfanin kera baturan Lithium da farantan wutar sola zai rinka samar da ribar dala buliyan dari 5 a duk shekara kamar dai yadda gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya tabbatar wanda kuma shi ne ya jagorancin ‘yan kasuwar ta kasar China zuwa fadar ta shugaban kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)