logo

HAUSA

An yi gadon tunanin iyalin shugaba Xi Jinping ta wata takardar rubuce-rubuce

2024-05-12 16:58:02 CMG Hausa

Mahaifiyar shugaba Xi Jinping Qi Xin ta taba yin rubuce-rubucen wasu maganganu a lokacin daular Ming ta kasar Sin, inda ta ce, “dalilin da ya sa ma’aikata suke girmama ni shi ne, ba na cin hanci da karbar rashawa, ba domin ina da tsattsauri ba, mutane sun yi imani da ni ne ba domin ina da kwarewa kan aiki ba, sai domin ina aiki cikin adalci. Idan na yi aiki cikin adalci, to ba za a cuci jama’a ba, idan ba na cin hanci da karbar rashawa, to, ma’aikata ba za su nuna lalaci ga aikinsu ba. Tabbatar da adalci zai kai ga tsara kuduri mai dacewa, kana hana cin hanci da karbar rashawa, zai kai ga samun girmamawa daga jama’a”.

Wadannan rubuce-rubuce masu ma’ana sun shaida tunanin iyalin shugaba Xi Jinping. Shugaba Xi yana tunawa da wadannan maganganun da mahaifiyarsa ta rubuta. A gun wani muhimmin taro, shugaba Xi ya taba tsamo wannan magana don gayawa dukkan membobin jam’iyyar Kwaminis ta Sin su tabbatar da adalci da hana cin hanci da karbar rashawa. Shugaba Xi ya yi kokarin kasancewa wani mutum mai samar da moriya ga jama’a ta hanyar koyi da tunanin iyalinsa. Ya taba ba da kyautar kudi ga wani dalibi mai fama da talauci har na tsawon shekaru 12 a jere don tabbatar da ya ci gaba da karatu, kana ya ziyarci wannan dalibi sau 8 da amsa wasikunsa sau 5, da zummar ba shi kwarin gwiwa. Yayin da yake aiki a garin Ningde, ya taba shiga kauyen Xiadang sau uku, da gina hanyoyin mota da tashar samar da wutar lantarki daga karfin ruwa a wurin. Bayan ya zama babban sakataren jam’iyyar, Xi Jinping ya bukaci dukkan membobin jam’iyyar su yi aiki a kauyuka, da aiwatar da ayyukan yaki da talauci, kuma karkashin jagorancinsa, kasar Sin ta kirkiro wani abun alajabi a tarihin yaki da talauci na dan Adam.

Xi Jinping ya kiyaye tunawa da wadanan maganganu, inda ya ce, ko da yake ana samu babban sauyi a zaman rayuwa ta wannan zamani, ya kamata a ci gaba da daukar iyali da tunanin iyali da muhimmanci. (Zainab Zhang)