logo

HAUSA

Xi Jinping ya nuna matukar godiya ga mahaifiyarsa

2024-05-12 17:04:27 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba karanta wakar “dan iyali zai bar gida”, wato mahaifiya tana dinkawa danta wanda zai bar gida riga. Tana kokarin dinkawa cikin hanzari saboda kada lokaci ya kure, kuma ba ta san yaushe zai koma gida ba. Shugaba Xi ya bayyana cewa, wannan waka ta shaida kaunar gida ta jama’ar kasar Sin.

Shugaba Xi Jinping yana bayar da muhimmanci matuka ga iyalinsa. A bikin murnar sabuwar shekara ta 2017, Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taba zuciya, inda ya ce, kada a manta da iyalai duk da tazara mai nisa dake akwai, da ma dimbin ayyukan da ake da su.

Ci gaban ko wanne gida yana ingiza ci gaban wata kasa, gudunmawar da kowane iyali ya bayar, zai hadu waje guda don zama karfi mai inganci na farfadowar al’ummar Sinawa baki daya. (Zainab Zhang)