Kasar Sin Ta Yi Bayanin Matsayarta Dangane Da Kudurin MDD Mai Lamba 2758
2024-05-12 21:10:10 CMG Hausa
Daraktan ofishin kula da harkokin arewacin Amurka da yankin Oceania na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Yang Tao, ya kira wani taron manema labarai, inda ya yi bayani game da matsayar kasar Sin don gane da kudurin MDD mai lamba 2758.
A cewar Yang Tao, Amurka ta dade tana jirkitawa tare da kalubalantar kudurin wanda aka zartas a shekarar 1971 da ke mayarwa kasar Sin halaltacciyar kujerarta a MDD tare da watsi da kungiyar Chiang Kai-shek.
Ya ce, da farko, manufar kasar Sin daya tak a bayyane take, wadda ke nufin kasar Sin daya ce tak a duniya kuma Taiwan wani bangare ne nata, kana gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce gwamnati daya tilo dake wakiltar kasar baki dayanta, yana mai cewa, kudurin na jaddada manufar kasar Sin daya tak a duniya.
Na biyu, kasashen duniya sun amince da kudurin, kuma suna aiwatar da shi bisa gaskiya. Kana kudurin, mataki ne da babban zauren MDD ya dauka, don haka ya kamata dukkan mambobi su amince da shi.
Na hudu, dole ne Amurka ta dakatar da jirkirtawa da lalata kudurin. Ya ce Sin na gargadin Amurka game da kudurin, yana mai cewa biyayya ga kudurin hakki ne da ya rataya a wuyanta, amma ba ta da hurumin jirkita shi, haka kuma ba ta da wani fifiko da zai ba ta damar yin yadda ta ga dama. (Fa’iza Mustapha)