logo

HAUSA

Xi Jinping ya kammala ziyarar aikinsa a Faransa da Serbia da Hungary ya kuma dawo birnin Beijing

2024-05-11 16:02:22 CMG Hausa

 A safiyar yau Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kammala ziyarar aikinsa a kasashen Faransa, da Serbia, da Hungary, ya kuma dawo birnin Beijing ta jirgin saman musamman.

Mai dakinsa Peng Liyuan, da kuma zaunannen wakilin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana darektan ofishin gudanarwa na kwamitin koli Mr. Cai Qi, da mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Mr. Wang Yi sun rufa masa baya yayin dawowa kasar Sin. (Amina Xu)