Wang Yi ya yi bayani kan ziyarar aiki da Xi Jinping ya gudanar a kasashen Turai uku
2024-05-11 16:05:22 CMG Hausa
Tsakanin ranakun 5 zuwa 10 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da ziyarar aiki a kasashen Turai guda uku, wadanda suka hada da Faransa, da Serbia, da kuma Hungary.
Dangane da ziyarar aikin a kasashen uku, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasa Wang Yi ya gabatar da karin bayani. Inda ya ce kasar Faransa kasa ce ta farko da ta kulla huldar diflomasiyya da Jamhuriyyar Jama’ar Kasar Sin cikin manyan kasashen yammacin duniya, kuma tana bin ka’idar ’yancin kai, da mulkin kai a ko da yaushe.
Wang Yi ya kara da cewa, ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping ya yi a kasar Faransa, ta kasance muhimmin mataki a jadawalin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin Sin da Faransa. A yayin ziyararsa a kasar, bangarorin biyu sun fidda sanarwar hadin gwiwa guda 4, wadanda suka hada da sanarwar hadin gwiwa kan yanayin Gabas ta Tsakiya, da sanarwar hadin gwiwa kan kare nau’o’in halittu da tekuna, da sanarwar hadin gwiwa kan ayyukan gona, da kuma sanarwar hadin gwiwa kan fasahar AI, da harkokin kasashen duniya. Ban da haka kuma, sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa kimanin guda 20.
Haka kuma, Wang Yi ya ce, kasar Serbia ita ce abokiyar hadin gwiwa manyan tsare-tsare ta farko ta kasar Sin a yankin Turai. Kuma a ’yan shekarun nan, shugaba Xi Jinping da shugaba Aleksandar Vucic sun kafa dangantakar fahimtar juna mai zurfi a tsakaninsu, bisa mu’amalar da suka yi, inda suka cimma nasarar raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin sauri, kuma kamar yadda ake fatan. A wannan karo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake yin ziyarar aiki a kasar Serbia bisa gayyatar da shugaba Vucic ya yi masa, inda shugabannin biyu suka cimma matsaya daya a fannin karfafa dunkulewar kasashen biyu cikin sabon zamani.
Sa’an nan kuma, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Hungary tana cikin kasashe dake kan gaba a saurin kafa huldar diflomasiyya da jamhuriyar jama’ar Sin. A bana, ake cika shekaru 75 da kafa huldar diflomasiyyar jakadanci a tsakanin kasashen biyu. Cikin wadannan shekarun da suka gabata, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta bunkasa yadda ya kamata, inda aka cimma nasarar karfafa fahimtar juna a fannin siyasa, yayin da kuma aka samu sakamako da dama, bisa hadin gwiwar dake tsakaninsu. Yanzu haka, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana cikin yanayi mai kyau, ta kuma kasance abin koyi a fannin raya sabon salon dangantaka tsakanin kasa da kasa.
Wang Yi ya kuma kara da cewa, shekarar 2025 mai zuwa, ita ce ta cika shekaru 50, da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU, kuma yanzu ana cikin muhimmin lokaci na ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin Sin da EU.
Ya ce, a birnin Paris na kasar Faransa, a lokaci guda shugaba Xi ya gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar EU Ursula von der Leyen tare. A yayin ganawarsu, Xi ya yi bayani mai zurfi kan dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, ya kuma bayyana cewa, a matsayin manyan karfi cikin kasashen duniya, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar EU tana yin muhimmin tasiri ga zaman lafiya, da zaman karko, da kuma wadatar kasashen duniya.
A lokacin ziyararsa, shugaba Xi Jinping ya yi musayar ra’ayoyi da shugabannin kungiyar EU, game da batutuwan dake shafar rikicin Ukraine, da rikicin dake tsakanin Isra’ila da Falesdinu, da ma sauran harkokin kasa da kasa dake janyo hankulan jama’ar kasashen duniya. Xi Jinping ya ce, kamata ya yi kasar Sin da kasashen Turai su hada kansu, wajen hana bazuwa, da ci gaban rikice-rikice, yayin da ake samar da damammakin yin shawarwari a tsakanin bangarorin da abun ya shafa, domin kare tsaron makamashi, da hatsi na kasashen duniya, da kuma tabbatar da yanayin zaman karko a fannin samar da kayayyaki a tsakanin kasashen duniya.
Da yake tsokaci kan rikicin Isra’ila da Falesdinu kuwa, shugaba Xi ya jaddada cewa, abu mafi muhimmanci a halin yanzu, shi ne tsagaita bude wuta cikin sauri bisa dukkanin fannoni, da samar da taimakon jin kai yadda ya kamata, kana, a aiwatar da “daftarin kafa kasashe biyu”, a matsayin hanyar da ta dace ta warware matsalar daga asali. Kasar Sin tana goyon bayan a kira taron shimfida zaman lafiya na kasa da kasa cikin sauri, domin inganta aikin warware matsalar Falesdinu cikin yanayin adalci, kuma bisa dukkan fannoni.
Wang Yi ya ce, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kare gaskiyar tarihi, da yanayin adalci da zaman lafiya, lamarin da ya sa Sin din ta samu amincewa, da yabo daga gamayyar kasa da kasa, yayin da take ba da muhimmiyar gudummawa a fannin kare zaman lafiya, da zaman karko tsakanin kasashen duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)