logo

HAUSA

Shugaban rikon kwarya a Chadi ya lashe babban zaben kasa

2024-05-10 11:20:14 CMG Hausa

 

Shugaban rikon kwarya a kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, ya lashe babban zaben kasar da aka gudanar a makon jiya, kamar dai yadda hukumar zaben kasar ANGE ta bayyana.

Deby, mai shekaru 40 a duniya, ya yi takara ne karkashin gamayyar jam’iyyu da dama, da aka yi wa lakabi da "For a United Chad", ya kuma lashe kaso 61.03 bisa dari na jimillar kuri’un da aka kada. Yayin da firaministan kasa Succes Masra ke biye da shi da kaso 18.53 bisa dari, na jimillar kuri’un.

Shugaban hukumar ta ANGE Ahmed Bartchiret ne ya bayyana sakamakon farko da yammacin jiya Alhamis, yana mai cewa, "Ya kamata dukkanin masu ruwa da tsaki su kwantar da hankulansu, musamman a wannan gaba mai muhimmanci ta renon jaririyar dimokaradiyya".

Bartchiret ya yi tsokacin ne, yayin bikin da aka nuna ta kafar talabijin daga birnin N'Djamena, fadar mulkin kasar, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati, da masu sanya ido a zaben, da sauran jami’an diflomasiyya.

Kafin bayyana sakamakon, firaminista Masra, ya bayyana ta sakon da ya wallafa a shafin Facebook, cewa alkaluman kidayar kuri’un da aka kada daga wakilansa, sun nuna shi ne ke kan gaba a zaben.

Nan gaba ake sa ran mika kwarya-kwaryar sakamakon ga majalissar kundin tsarin mulkin kasar, wadda za ta bayyana sakamakon karshe na zaben kafin ranar 5 ga watan Yuni.    (Saminu Alhassan)