logo

HAUSA

Mutane biliyan 1.3 za su yi fama da ciwon sukari a shekarar 2050

2024-03-11 18:41:26 CMG Hausa

 

Wani nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2050, yawan masu fama da ciwon sukari a fadin duniya zai karu zuwa biliyan 1.3, kana yawan masu fama da ciwon a dukkan kasashe za su karu.

Wannan nazarin da kwalejin kula da ma’aunin lafiya da kimantawa karkashin shugabancin jami’ar Washington ta kasar Amurka ya gudanar, ya nuna cewa, a shekarar 2021, mutane miliyan 529 ne suke fama da ciwon na sukari a duk fadin duniya, ciki had da wasu kashi 96 cikin 100 dake fama da ciwon nau’i na 2. Akwai wata alaka a tsakanin ciwon sukari mai nau’i na 2 da kuma matsalar nauyin jiki da ya wuce misali da rashin isasshen motsa jiki. Kana za a iya rage barazanar kamuwa da ciwon ta hanyar yin zaman rayuwa yadda ya kamata.

Nazarin ya shaida cewa, nan da shekaru kusan 30 masu zuwa, yawan masu fama da ciwon sukari nau’i na 2 zai karu, sakamakon karuwar yawan masu kiba da dai sauransu, lamarin da zai haifar da karuwar yawan masu fama da ciwon sukari.

Yanzu yawan masu fama da ciwon sukari bisa jimillar dukkan al’ummun duniya ya kai kashi 6.1 cikin kashi 100. A arewacin nahiyar Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya kuma, adadin ya fi yawa, inda ya kai kashi 9.3 cikin kashi 100. A cikin mutane masu mabambantan shekaru kuma, ‘yan tsakanin shekaru 75 zuwa 79 ne aka fi samun adadi mafi yawa na masu fama da ciwon sukari, inda adadin ya kai kashi 24.4 cikin kashi 100.

Yanzu haka, a kasashe da yankuna masu karanci da matsakaicin kudin shiga, masu fama da ciwon sukari da yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi 10 ne suke samun kulawa yadda ya kamata. Ya zuwa shekarar 2045, masu fama da ciwon na sukari da yawansu ya kai kashi 3 cikin kashi 4 ne suka fito daga wadannan kasashe da yankuna.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, saurin karuwar yawan masu fama da ciwon sukari ya wuce zaton mutane matuka, kuma hakan ya haifar da kalubale ga tsarin kiwon lafiyar al’ummar kasa da kasa. Don haka wajibi ne kasashen duniya su fito da shiri na dogon lokaci da zuba isasshen kudade da kuma sanya kulawa sosai kan yaki da ciwon na sukari. (Tasallah Yuan)