logo

HAUSA

Sauyin yanayi ya kawo tsaiko kan dakilewa da kandagarkin cutar AIDS, tarin fuka da ciwon zazzabin sauro

2024-02-27 10:35:44 CMG Hausa

 

Peter Sands, babban darektan zartaswa na gidauniyar yaki da cutar AIDS da tarin fuka da ciwon zazzabin sauro na duniya ya yi kashedi a kwanan baya da cewa, sauyin yanayi da rikice-rikicen masu dauke da makamai suna illata kokarin da kasashen duniya ke yi na yaki da wadannan munanan cututtuka masu yaduwa.

Rahoton da gidauniyar ta gabatar a kwanan baya ya nuna cewa, an maido da ayyukan duniya na dakile da kandagarkin wadannan cututtuka 3 yadda ya kamata. Amma a cikin wata sanarwar da aka bayar a lokaci guda kuma, mista Sands ya yi nuni da cewa, sauyin yanayi da rikice-rikicen masu dauke da makamai suna kara haifar da barazana. kuma idan ba a dauki matakai ba, to, ba za a cimma manufar kau da cututtukan 3 baki daya daga duniya a shekarar 2030 ba.

Alal misali, yanzu haka ciwon zazzabin sauro ya yadu a wasu wuraren Afirka da ke kan tudai, inda ba zafi. Yanayin wadannan wurare bai cancanci sauro masu dauke da kwayoyin cutar ciwon zazzabin sauro su rayu ba. Haka zalika, a wasu sassan kasa da kasa, ambaliyar ruwa da sauran yanayi masu tsanani sun haddasa rushewar asibitoci, rabuwar al’umma da muhallansu, karuwar yawan wadanda suka kamu da wadannan cututtuka 3, da dakatar da ba da jinya ga masu fama da cututtukan. A kasashen Sudan da Afghanistan da wasu kasashe da yankuna, rashin kwanciyar hankali ya kawo tsaiko ga yunkurin isa wuraren da ke matukar bukatar taimako.

Mista Sands ya ci gaba da cewa, an samu kyakkyawan ci gaba wajen dakilewa da kandagarkin cutar AIDS, tarin fuka da ciwon zazzabin sauro a duniya. A shekarar 2022, mutane miliyan 6 da dubu 700 masu fama da tarin fuka ne suka samu jinya a kasashe da yankunan da gidauniyarsa ta zubawa jari, adadin da ya karu da miliyan 1 da dubu 400 bisa na shekarar 2021, inda ya kafa sabon tarihi. Haka zalika kuma, gidauniyar ta taimakawa mutane miliyan 24.5 masu dauke da kwayar cutar AIDS samun jinya, tare da rarraba gidajen sauro miliyan 220 ga al’umma. (Tasallah Yuan)