logo

HAUSA

Masana na ganin rashin isasshen barci zai iya kara wa dan Adam barazanar kamuwa da ciwon sukari

2024-03-08 08:07:58 CMG Hausa

 

Nazarce-nazarce guda 2 da aka gudanar a kasar Amurka sun shaida mana cewa, da alamun rashin isasshen barci zai iya kara wa mu ‘yan Adam barazanar kamuwa da ciwon sukari.

Masu nazari daga jami’ar Colorado ta kasar Amurka sun kaddamar da rahoton nazarin da suka yi a kwanan baya, kan masu koshin lafiya 16 wadanda shekarunsu suka wuce 20 amma ba su kai 25 a duniya ba. Masanan sun raba wadannan mutane zuwa rukunoni guda biyu. Rukuni na farko an sa su yi barci na tsawon awoyi biyar da dare a kwanaki 5 a jere, kana bayan kwanaki 5 a jere, sai suka yi awoyi 9 suna barci da dare. Yayin da su kuma rukuni na biyu suka yi sabanin hakan.

Binciken jininsu ya nuna cewa, idan har dukkan wadannan matasa 16 suka yi barci na tsawo sa’o’i 5 da dare, to, yawan sukari dake cikin jininsu zai ragu, idan kuma hakan ya ci gaba, to, alamu sun nuna cewa, za su iya fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sukari. Duk da haka nazarin ya shaida cewa, idan an tsawaita lokacin barcinsu zuwa sa’o’i 9, to, yadda aka daidaita yawan sukarin a cikin jininsu ya kan koma yadda ya kamata.

Mene ne dalilin haka? Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin haske da cewa, rashin isashen barci kan hana sassan da ke sarrafa kwakwalwar bil Adama yin aiki yadda ya kamata. Idan mutane suka tashi daga barci da wuri, amma sassan kwakwalwarsu ba ta gama wartsakewa ba, akwai yawan sinadarin Melatonin wanda ke sanya jikin mutum jin barci. A daidai wannan lokaci, idan sun ci abinci a maimakon su yi barci, to, tabbas, jikinsu yana kara samar da sinadarin Insulin domin tabbatar da daidaiton sukarin da ke cikin jininsu, idan mutanen suka dade suna yin hakan, to, jikinsu ba zai iya jurewa ba, sannu a hankali sai jikinsu ya kasa daidaita yawan sukari da ke cikin jininsu.

Ban da haka kuma, jami’ar Harvard ta Amurka da wasu hukumomi sun gudanar da wani nazari na daban kan mata kusan dubu 60 wadanda shekarunsu suka wuce 55 da haihuwa, inda suka gano cewa, idan mata tsoffafi da masu matsakaitan shekaru suka shafe awoyi fiye da 8 suna barci a ko wane dare, ko kuma tsawon lokacin barcinsu bai kai awoyi 6 a ko wace rana ba, to, barazanar da suke fuskanta ta kamuwa da cutar sukari nau’i na 2 kan karu. Matan da suke fuskantar barazanar kamuwa da cutar mafi kankanta su ne wadanda suke barci na fiye da awoyi 7 amma bai kai 8 ba a ko wace rana. A takaice dai, barci mai tsawo ko kuma rashin isasshen barci dukkansu na iya haifar da illa ga lafiyar bil Adam.   (Tasallah Yuan)