logo

HAUSA

Matasa masu fama da ciwon sukari sun fi saurin kamuwa da cutar damuwa

2024-03-19 11:18:48 CMG Hausa

 

Masu nazari daga kasar Australiya sun yi nuni da cewa, akwai wata alaka tsakanin karuwar yawan masu fama da ciwon sukari mai nau’in 2 da kuma karuwar yawan masu fama da cutar damuwa, musamman tsakanin matasa.

Masu nazarin sun tantance takardun tarihin ganin likita na ‘yan kasar Birtaniya dubu 230, sun gano cewa, a shekarar 2017, wasu kashi 43 cikin kashi 100 na masu fama da ciwon sukari mai nau’in 2 sun kamu da cutar damuwa. Adadin ya kai kashi 29 cikin kashi 100 a shekarar 2007.

Haka kuma, in an kwatanta su da wadanda suka kamu da ciwon sukari mai nau’in 2 bayan shekarunsu sun wuce 50 a duniya, wadanda suka kamu da ciwon kafin shekarunsu su kai 40 a duniya sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar damuwa har kashi 50 cikin kashi 100. A cikin matasa masu fama da ciwon sukari, wasu da yawa suna fama da matsalar kiba mai muni, lamarin da ya kan haifar da illa ga tunaninsu.

A cikin dogon lokaci da ya wuce, ana daukar ciwon sukari kamar wani nau’in ciwon da masu matsakaitan shekaru su kan kamu da shi. A kasar Birtaniya, matsakacin shekarun masu kamuwa da ciwon ya kai 58 a duniya. Amma a shekaru kusan 20 da suka wuce, zaman rayuwa ta hanyar da ba ta dace ba, ya sanya yawan masu fama da ciwon ya ninka sau 1 a Birtaniya. A cikin dukkan masu kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2 a shekarar 2017, wasu kashi 12.5 cikin kashi 100 ne shekarunsu ba su kai 40 a duniya ba. Adadin ya karu da kashi 1 cikin kashi 3 bisa na shekarar 2000.

Masu nazarin daga kasar Australiya sun yi bayani da cewa, nazarinsu ya gano alakar da ke tsakanin kamuwa da ciwon sukari da matasa suka yi da kuma lafiyar tunaninsu, ya kuma nuna cewa, yin rigakafin kamuwa da ciwon sukari yana da ma’ana mai muhimmanci.

Dangane da hakan, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, wajibi ne a kara ba da muhimmanci ga alakar da ke tsakanin ciwon sukari da kuma cutar damuwa. Ciwon sukari yana illata lafiyar jiki, amma an dade ba a mai da hankali kan illolin da yake haifarwa kan tunani. (Tasallah Yuan)