logo

HAUSA

Ko da hasken fitila kalilan ne, yana iya yin illa ga yawan sukari dake cikin jinin bil Adama

2024-03-31 19:26:47 CMG Hausa

 

Masu karatu, ko kuna barci da dare, amma ba ku kashe telebijin ko fitila ba? Ko kun san cewa, hakan zai iya hana ku samun isasshen barci, tare da kawo tsaiko kan yadda ake tabbatar da daidaiton yawan sukari a cikin jinin bil Adama yadda ya kamata?

A baya, masu nazari sun gano cewa, wasu su kan yi barci da dare, ba tare da kashe fitila ko telebijin ba. Wadannan mutane su kan yi fama da matsalar kiba ko kamuwa da ciwon sukari mai nau’in 2. Amma nazarin bai tabbatar da cewa, haske ne ya haifar da wannan matsala ba.

Masu nazari daga kwalejin horas da likitoci na Feinberg, reshen jami’ar Northwestern ta kasar Amurka sun gudanar da nazari kan wannan lamari, inda suka gayyaci masu aikin sa kai masu koshin lafiya 20 su kasance cikin dakin gwaje-gwaje dangane da harkokin barci har dare guda 2. A dare na farko dukkan masu aikin sa kan sun yi barci a daki mai duhu, amma a dare na biyu, rabinsu sun yi barci, ba tare da kashe telebijin ko fitila ba.

A safiyar kwana na uku, masu nazarin sun yi bincike kan yawan sukari da ke cikin jinin masu aikin sa kan. Masu nazarin sun binciko yawan sukarin da na sinadarin insulin da ke cikin jininsu bayan sun farka daga barci, da kuma binciken yawan sukari da ke cikin jinin masu aikin sa kan bayan sun sha ruwan glucose.

Sakamakon binciken ya nuna cewa, yadda masu aikin sa kan suke sarrafa yawan sukari da ke cikin jininsu a dare na farko inda suka yi barci a cikin daki mai duhu, ya fi yadda suka yi barci a daki mai haske kadan a dare na biyu. Masu nazarin sun yi karin haske da cewa, ko da yake masu aikin sa kan suna zaton cewa, haske kadan din da ke cikin dakinsu bai hana su yi barci da kyau ba, amma kwakwalwarsu na ganin cewa, ba su kashe telebijin ko fitila ba.

Duk da haka, masu nazarin sun yi nuni da cewa, kafin a samu sakamakon binciken da za a gudanar kan mutane masu yawa kan wannan batu, bai kamata ba mutane su sauya al’adarsu ta yin barci. (Tasallah Yuan)