logo

HAUSA

Manoman sassan kasar Sin sun fara aikin girbi na lokacin zafi

2024-05-16 20:30:21 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, barka da war haka. Yanzu, lokacin girbin hatsi ne na lokacin zafi a nan kasar Sin. Manoma sun fara girbin alkama a wurare daban daban, suna amfani da fasahohin zamani, da injunan aikin gona wajen gudanar da ayyuka masu nasaba da hakan, domin tabbatar da samun hatsi mai yawa.