logo

HAUSA

Sin da Hungary sun daukaka dangantakarsu zuwa ta abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni

2024-05-10 01:05:14 CMG

Shugaban kasar Sin Xi Jinping dake ziyarar aiki a Hungary, ya tattauna da yammacin ranar Alhamis da firaministan kasar Viktor Orban, a ofishin firaministan dake birnin Budapest. Shugabannin biyu sun sanar da cewa, Sin da Hungary sun daukaka dangantakar dake tsakaninsu zuwa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a sabon zamani. 

Bayan tattaunawar, shugabannin kasashen biyu sun shaida yadda aka yi musayar wasu takardu na hadin gwiwa a fannonin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da tattalin arziki da cinikayya, da zuba jari da kimiyya da fasaha da al'adu da noma da dai sauransu, kana sun gana da manema labaru tare.

Baya ga haka, shugabannin biyu sun kuma fitar da hadaddiyar sanarwa game da daukaka dangantakar dake tsakanin kasashensu zuwa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a sabon zamani, da ma wasu takardun da suka shafi nasarorin da aka cimma yayin ziyarar. (Fa’iza Mustapha, Bilkisu Xin)