logo

HAUSA

Xi Jinping da firaministan Hungary sun gana da manema labaru

2024-05-10 05:50:29 CMG

Da yammacin jiya Alhamis, 9 ga wata bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Hungary Viktor Orban sun gana da manema labarai, bayan ganawar da suka yi a ofishin firaministan dake birnin Budapest.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ya yi tattaunawa mai inganci, da sada zumunci da firaminista Orban, inda suka yi musayar ra'ayi mai zurfi kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Hungary a sabon zamani, da batutuwan dake jan hankalin bangarorin biyu, kuma sun cimma matsaya daya a fannoni daban daban. Baya ga haka, sun shaida yadda aka yi musayar jerin muhimman takardun hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, kasar Sin tana ba da cikakken goyon baya ga gina kasa mai karfi da farfado da al’umma bisa salon da ta zaba na zamanantar da kanta. Ya ce zamanantarwa irin ta kasar Sin za ta kawo manyan damammaki ga duniya. Kuma kasar Sin tana son samun ci gaba da wadata tare da kasar Hungary.

A nasa bangaren, firaminista Orban ya ce, kasar Hungary tana goyon bayan jerin shawarwarin kyautata harkokin duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, kuma ta amince da shirye-shiryen kasar Sin na sa kaimi ga warware rikicin shiyya-shiyya cikin lumana, ciki har da rikicin Ukraine.(Bilkisu Xin)