logo

HAUSA

Kenya Ta Karbi Bakuncin Baje Kolin Hada-hadar Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Afirka

2024-05-10 10:58:31 CMG Hausa

An kaddamar da taron baje kolin harkokin da suka shafi raya tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka ko CAETE, na shekarar nan ta 2024 a birnin Nairobin kasar Kenya, a gabar da hada-hadar kasuwanci, da zuba jari tsakanin sassan biyu ke kara fadada.

Baje kolin na yini uku wanda aka bude a jiya Alhamis, ya hallara babbar tawaga daga lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin.

Da take tsokaci game da hakan, babbar sakatariya a ma’aikatar bunkasa zuba jari, cinikayya da raya masana’antu ta Kenya Rebecca Miano, ta ce baje kolin na wannan karo, shaida ce ta irin dogon tarihin hadin gwiwa da kawance dake wakana tsakanin Sin da kasashen Afirka.

A nasa bangare kuwa, shugaban hukumar bunkasa cinikayya da masana’antu na kasar Eric Rutto, cewa ya yi baje kolin alama ce ta irin ci gaban da aka samu, wanda kuma zai ingiza Sin da kasashen Afirka ga cimma nasarar inganta takarar su, da samun ci gaba mai dorewa.

Rutto ya kara da cewa, baje kolin ya samar da wata dama mai muhimmanci ta bude sabon babin cudanya, da hadin kai tsakanin jagororin masana’antu, da masu zuba jari, da masu fatan yin hadin gwiwa a nan gaba. Ya kuma share fagen cin gajiya daga juna, wadda ka iya bunkasa tattalin arzikin sassan.    (Saminu Alhassan)