logo

HAUSA

Ecowas na shirye-shiryen kaddamar da dakarun kota-kwana da za su yaki ta’addanci a Najeriya da makwaftan kasashe

2024-05-10 09:49:13 CMG Hausa

Kungiyar Ecowas na shirye-shiryen samar da dakarun tsaron kota-kwana da za su taimakawa Najeriya da sauran kasashen makwafta wajen yaki da ayyukan ta’addanci.

Kwamishinan lura da harkokin siyasa da tsaro na kungiyar Ambasada Abdel-Fatau Musah ne ya tabbatar da hakan yayin taron tuntuba na yini uku da aka shiryawa manyan jami’an cibiyoyin bayar da horo a kan tsaro da shugabanci na kasashen dake cikin kungiyar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ambasada Abdel-Fatau Musah ya bayyana damuwar kungiyar ta Ecowas a game da yadda ayyukan ta’addanci ke ci gaba da wanzuwa a yankin Sahel, inda ya tabbatar da kudurin kungiyar na tara tsabar kudi har dala biliyan 2.4 domin samar da dakarun tsaron musamman.

Ya ce, abin takaici yanzu kasar Burkina Faso ta maye gurbin Afghanistan a matsayin yankin da ayyukan ’yan ta’adda ya fi kamari a duniya, kuma yanzu haka nahiyar Afrika ita ta fi yawan kungiyoyin ’yan ta’adda a duniya baki daya.

“Muna aiki kafada da kafada da kungiyar tarayyar Afrika a kan wannan batu domin tabbatar da ganin mun kiyaye hakkin dan adam a dukkannin abun da za mu yi.”

A jawabinsa kwamandan kwalejin horas da dakarun tsaro ta Najeriya Rear Admiral Olumuyiwa Olotu ya ce, babu shakka matakin kungiyar ta Ecowas zai kara karsashi sosai ga dakurun tsaron Najeriya ta fuskar yaki da ’yan ta’adda.

“Kwalejin horas da dakarun tsaro na kasa zai yi kokarin sauke nauyin da aka dora masa ta hanyar shirye-shirye da tarukan karawa juna sani da bayar da horo da kuma aikin hadin gwiwa.” (Garba Abdullahi Bagwai)