logo

HAUSA

An samu sabuwar damar kyautata hulda tsakanin Sin da Hungary

2024-05-10 16:24:19 CMG Hausa

“Ziyarar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ta kai kasarmu tana cike da ma’anar tarihi.” In ji Viktor Orban, firaministan kasar Hungary, yayin da yake hira da wakilin CMG a jiya Alhamis. Amma ko me ya sa ya ce tana da ma’anar tarihi? Saboda ziyarar shugaban ta haifar da dimbin sakamako.

Yayin wannan ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai kasar Hungary, shugabannin kasashen 2 sun gabatar da hadaddiyar sanarwa, inda suka sanar da daga matsayin huldar dake tsakanin kasashen 2, daga huldar abota da ta shafi manyan tsare-tsare a dukkan bangarori, zuwa wata mai alaka da sabon zamani, wadda za ta jure duk wani mawuyacin hali.

Manazartan al’amuran kasa da kasa na ganin cewa, wannan ci gaba ya nuna cewa, wasu harkoki na huldar dake tsakanin kasashen 2, da suka hada da amincewa da juna ta fuskar siyasa, da matsaya daya da suka cimma bisa manyan tsare-tsare, da hadin kansu a kokarin daidaita wasu al’amura, dukkansu za su cimma wani sabon matsayi. Kana huldar dake tsakanin kasashen 2 za ta iya jure duk wani kalubale, a duk wani yanayin al’amuran kasa da kasa. Ban da haka, kasashen 2 sun kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa fiye da 10, wadanda suka aza harsashi ga yunkurin habaka hadin kan kasashen 2 a nan gaba.

Wani abun lura shi ne, Mista Orban ya musanta zargin da aka yi wa kasar Sin, cewa wai akwai “matsalar yawan samar da kayayyaki fiye da kima” a kasar, da “bukatar kawar da hadari” a kasar, da dai sauransu. A ganinsa, ci gaban kasar Sin dama ce ga tattalin arzikin kasashen Turai, maimakon kalubale mai hadari. Maganarsa ta nuna gaskiya da sanin ya kamata, da niyyar kasar Hungary ta zurfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin.

Za mu iya hangar yadda kasashen Sin da Hungary za su hada gwiwarsu a kokarinsu na tabbatar da zamanantarwar kasa, da neman samun ci gaba da walwala tare, abun da zai taimaki yunkurin zurfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen gabashin nahiyar Turai na tsakiya. (Bello Wang)