logo

HAUSA

Shenzhen ya kyautata manhajar ba da hidima domin biyan bukatun baki

2024-05-09 15:41:29 CMG Hausa

 

Kwanan baya, manhajar “i Shenzhen” da aka shigar da sabbin sassa 9 na harsunan Turanci, Japananci, Faransanci, Larabci, Rashanci, Jamusanci, da na kasashen Koriya ta Kudu, Spain da Portugal, ta fara aiki, wadda take ba da hidimomin gwamnati.

Yanzu haka mahukuntan Shenzhen da ke kudancin kasar Sin suna ba da hidima cikin wasu harsunan waje a yanar gizo da kuma wayar salula, a kokarin ganin kamfanoni masu jarin waje da baki sun samu sauki ta fuskar gudanar da ciniki, zuba jari, samun aikin yi, samun wurin kwana, yin yawon bude ido a birnin na Shenzhen. Daga nan ne ake samun damar yin duba, yin oda, da daidaita batutuwa masu muhimmanci dake da alaka da baki a yanar gizo ko ta wayar salula, ta yadda kamfanoni masu jarin waje da baki za su kara sanin Shenzhen da ji dadin zama a birnin cikin gajeren lokaci. (Tasallah Yuan)