Xi Jinping ya halarci liyafar ban kwana da Vucic da mai dakinsa suka shirya
2024-05-09 01:33:10 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da mai dakin sa Peng Liyuan, sun halarci liyafar ban kwana da shugaban kasar Serbia Aleksandar Vucic da mai dakin sa Tamara Vucic suka shirya a birnin Belgrade a ranar Laraba.