logo

HAUSA

Shugaban kasar Benin ya tabbatar da hana ficewa da gurbataccen man fetur din Nijar ta Seme Krake

2024-05-09 16:27:30 CMG Hausa

A jamhuriyyar Benin, shugaban kasar Patrice Talon ya tabbatar a ranar jiya Laraba 8 ga watan Mayun shekarar 2024, da matakin hana ficewar gurbataccen man Nijar tashar ruwan Seme Kpodji.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu ya aiko mana da wannan rahoto. 

 

A cikin wata sanarwa, Patrice Talon ya bayyana damuwa kan yadda dangantaka ke tsami tsakanin kasashen biyu tare da jaddada cewa yana fatan kome zai daidaita.

Shugaba Patrice Talon ya dauki magana domin tabbatar da yin bayani da ba da dalilinsa na daukar wannan mataki. Ya kuma nuna damuwa kan shirin hukumomin Nijar kan kokarinsa na sulhunta rikici da daidaita huldar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu. Ya yi raskunan kan hanyoyin da ya bi domin daidaita matsalar, kamar bude iyakoki daga bangaren Benin, aika sakwanni, har ma da tura ministan harkokin wajensa a birnin Yamai a matsayin wani manzon musamman.

Shugaban kasar Benin yana ganin cewa, ya kamata musanya tsakanin kasashen biyu ta kasance a hukumance kuma bisa tsari. Haka zalika, ya nuna cewa yawan hatsin da ke shiga Nijar ya sabawa doka, bai kamata a dauke mu a matsayin abokan gaba ba kuma a nemi yin aiki tare da mu, in ji Patrice Talon.

Domin dage wannan mataki, shugaban Benin ya aza sharudansa, idan hukumomin Yamai suka amince ba da hadin kai, jiragen ruwan dakon dayen man Nijar za su ratsa ruwan kasar Benin.

Shugaba Patrice Talon dai na neman a bude iyakokin kasa domin maido da huldar dangantaka.

“Ina nuna damuwa matuka kan yadda dangantaka tsakanin Nijar da Benin ta yi zafi, alhali kasashe ne abokai, ’yan uwan juna, amma daukar Benin a matsayin abokiyar gaba, da bayyana cewa ta jigbe sojojin kasashen waje domin kai ma Nijar hari, abu ne da hankali bai dauka”, in ji shugaban kasar Benin.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.