logo

HAUSA

Darajar cinikayyar waje ta Sin ta karu da kaso 5.7 a watanni hudu na farkon bana

2024-05-09 19:41:52 CMG Hausa

Jimillar hajojin da aka yi hada hadar shigowa, da wadanda aka fitar daga Sin sun karu da kaso 5.7 bisa dari a shekara, a kudin kasar yuan, cikin watanni hudu na farkon shekara bana.

Wasu alkaluman hukumar kwastam ta kasar Sin ne suka tabbatar da hakan a yau Alhamis, inda suka nuna karuwar hajojin fitarwa kasashen waje da kaso 4.9 tsakanin watan Janairu zuwa Afirilun bana, in an kwatanta da na shekarar bara, yayin da karuwar hajojin da ake shigowa da su kasar ta Sin ya daga da kaso 6.8 bisa dari a tsakanin wa’adin.  (Saminu Alhassan)