logo

HAUSA

Shugaba Xi: Har kullum Sin da Hungary na kallon alakar su daga mahanga mai fadi da wa’adi mai tsawo

2024-05-09 05:27:04 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce ya yi imani duk yadda aka samu sauye sauye a harkokin kasa da kasa, kasarsa da Hungary za su ci gaba da kallon alakar su daga mahanga mai fadi a kuma tsawon lokaci.

Shugaba Xi ya yi wannan tsokaci ne a ranar Laraba, cikin rubutaccen jawabin da ya gabatar yayin da ya sauka a kasar Hungary, inda ya fara gudanar da ziyarar aiki.   

Har ila yau, shugaban na Sin ya ce kasarsa da Hungary kawaye ne na hakika, kuma abokai na gari da suka amince da juna. Ya ce a bana ake cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, wanda hakan ya kawo muhimmiyar dama ta bunkasa alakar su.

Bugu da kari, shugaba Xi ya ce yana fatan ganawa da shugaba Tamas Sulyok, da firaminista Viktor Orban da sauran wasu jagororin kasar ta Hungary, tare da hada kai da su wajen shata sabon tsarin hadin gwiwa da samar da ci gaba, da nufin dora alakar kasashen biyu kan turbar babban ci gaba, da daga matsayin ta zuwa mataki na gaba. (Saminu Alhassan)