logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Hungary

2024-05-09 20:51:22 CMG Hausa

A safiyar yau Alhamis, bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping dake ziyarar aiki a kasar Hungary, ya gana da shugaban kasar Hungary Tamas Sulyok, a fadar shugabancin kasar dake birnin Budapest.

Yayin ganawarsu, Xi Jinping ya ce, yanzu haka kasar Sin na kokarin raya kai, da farfado da al’umma, ta salon zamanantarwa irin nata, wanda ke samar da dimbin damammaki na samun ci gaba ga duk duniya. Sin na son ganin abokananta na kasar Hungary sun ci gajiyar damammakin. Za ta kuma so zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa tare da bangaren Hungary, da hada zamanantarwar kasar Sin da manufar bude kofa ga gabashin duniya ta kasar Hungary waje guda, da habaka hadin gwiwar dake samar da hakikanin sakamako, da karfafa cudanya a karin fannoni. A cewar Xi, ta la’akari da yadda aka cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Hungary a wannan shekara da muke ciki, kasar Sin na son yin kokari tare da bangaren Hungary, wajen ganin huldar dake tsakanin kasashen 2 ta kara samun ingantuwa a kai a kai.

A nasa bangare, shugaba Sulyok na kasar Hungary, ya godewa shugaba Xi Jinping na kasar Sin, bisa shawarar raya “Ziri Daya da Hanya Daya” da ya gabatar, wadda ta sa kasar Hungary samun dimbin alfanu, bisa yadda aka gina karin kayayyakin more rayuwa, gami da hada su, don ba da karin damammaki na cudanya. A cewar shugaban na kasar Hungary, shugaba Xi ya gabatar da shawarwari na tabbatar da ci gaba, da tsaro, da daukaka wayewar kai da al’adu a duniya, gami da bukatar karfafa cudanya da hadin kai tsakanin mabambantan kasashe. Hakan, a cewar shugaba Sulyok, yana da matukar muhimmanci ga yunkurin daidaita matsalolin da kasashen duniya suke fuskantar, da magance taho-mu-gama tsakanin rukunai daban daban. Saboda haka, kasar Hungary ta yarda da shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar, tare da fatan karfafa cudanya tare da kasar Sin, da kara kokarin hada tsare-tsaren raya tattalin arziki na kasashen 2 waje guda, da sa kaimi ga gudanar wasu manyan ayyuka da ake hadin gwiwa a kai, ciki har da wani sabon layin dogon da zai hada Hungary da Serbia, ta yadda karin al’umma za su amfana. (Bello Wang)