logo

HAUSA

’Yan kasar Chadi dake jihar Borno su 3,500 ne suka samu damar kada kuri’ar su a zaben shugaban kasarsu

2024-05-08 10:15:02 CMG Hausa

’Yan kasar Chadi dake zaune a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya su 3,500 ne suka fita domin kada kuri’ar su a zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Litinin da ta gabata.

’Yan Chadin sun gudanar da zaben ne a harabar karamin ofishin jakadancin kasar dake birnin Maiduguri, sun kuma fara gudanar da zaben ne tun daga ranar Lahadi 5 ga wata har zuwa ranar Litinin 6 ga wata.

Ko da yake wannan ba shi ne karo na farko ba da ’yan kasar ta Chadi dake kasashen waje ke gudanar da zaben shugaban kasa ba, amma a nan Najeriya zaben na wannan lokaci ya fi daukar hankali sakamakon adadin ’yan kasar ta Chadi da suka fito domin kada kuri’arsu musamman a jihohin Kano da Legos da kuma birnin Abuja baya ga jihar ta Borno inda take da yawan mutane ’yan kasar Chadi.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai babban jami’i mai lura da karamin ofishin jakadancin kasar Chadi a jihar borno Dr. Umar Attaib ya ce, masu zaben dai sun nuna halin dattako yayin zaben, wanda wannan ya taimaka wajen samun nasarar zaben kamar yadda ake bukata.

“Mun sami taimakon jami’an tsaro kama daga bangaren ’yan sanda da hukumar shige da fice da kuma jami’an tsaron DSS, dukkanninsu sun yi aikin su sosai. Babu wata matsala, kuma alhamdulillahi yanzu sakamakon dake hannunmu na wucin gadi duk da ba ni da karfin ikon sanar da waye ya samu nasara a gaba dayan zaben kasar. Wajibi ne sai mu jira an kammala hada alkaluma gaba daya.”

Daga karshen ya yaba matuka bisa damar da gwamnatin kasar ta Chadi ta baiwa ’yan kasar Chadi dake kasashen waje na gudanar da zabe daga duk inda suke a duniya. (Garba Abdullahi Bagwai)