logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Taya Shugaba Putin Na Rasha Murnar Fara Sabon Wa’adin Mulki

2024-05-08 21:40:54 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, kasar na taya Vladimir Putin na kasar Rasha murnar shan rantsuwar kama aiki a wani sabon wa’adin mulki, kuma ta yi amana karkashin shugabancinsa, kokarin kasar na raya tattalin arziki da zamantakewa zai ci gaba da samun sabbin nasarori.

Kakakin ma’aikatar Lin Jian ne ya bayyana haka a yau Laraba, inda ya ce, karkashin shugabancin Xi Jinping da Vladimir Putin, an raya dangantaka mai karko da aminci tsakanin Sin da Rasha. Ya ce, bangarorin biyu za su bi matsayar da shugabanninsu suka cimma tare da ci gaba da inganta aminci da juna da fadada hadin gwiwarsu da raya abota da hada hannu wajen inganta samar da adalci da tsari a duniya da dunkulewar tattalin arzikin duniya da aiwatar da hadin gwiwa na hakika da kuma jagorantar duniya zuwa hanyar da ta dace, kuma mai tabbatar da adalci. (Faiza Mustapha)