Ziyarar Shugaba Xi A Serbia Ta Haifar Da Dimbin Nasarori
2024-05-08 22:19:17 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping na ziyarar aiki a kasar Serbia daga ranar 7 zuwa 8 ga wata. Yayin ziyarar, kasashen biyu sun sanar da zurfafawa da karfafa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakaninsu da kuma yunkurin gina al’umma mai makoma ta bai daya ga Sin da Serbia a sabon zamani. An kuma cimma ko rattaba hannu kan daftarorin hadin gwiwa 28 tsakanin kasashen biyu. (Fa’iza)