logo

HAUSA

Kasar Sin Ba Ta Da Matsalar “Samar Da Kayayyaki Fiye Da Kima”

2024-05-08 10:05:04 CMG Hausa

A baya-bayan nan dai, kasar Amurka da wasu sauran kasashen yamma sun yi ta yada labarin karya na cewar kasar Sin na “samar da kayayyaki fiye da kima", suna zargin kasar da "mamaye" kasuwannin duniya da kayayyakin sabbin makamashi masu arha, a cewarsu. Wannan zargi dai ya yi watsi da bukatun kasuwa, da kuma karfin sabbin masana'antar makamashi ta duniya. Ya ci karo da dokar tattalin arziki da ka'idojin cinikayyar na kasa da kasa. Kuma sun san da hakan, ko da yake ba tun yau aka fara irin wannan takaddamar ba, Sama da shekaru 20 da suka gabata, jim kadan bayan shigar kasar Sin cikin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, wasu suka fara kallon fitar da kayayyaki masu inganci a cikin farashi mai rahusa zuwa kasashen waje da take yi a matsayin barazana. Kazalika, Ba su yi nasarar kirar da suka yi ga kasashen duniya da su “raba gari da Sin” a kwanan baya ba, yanzu wannan batu na “samar da kayayyaki fiye da kima” shi ne suke yayatawa a matsayin wani sabon salon yakin cacar baka.  

Tabbas wannan zargi na dauke da manufar siyasa duba ga yadda kasar Sin a cikin kwanakin nan ta himmatu wajen zurfafa sauye-sauye ga manufofi masu ma’ana don kara bunkasa kasar musamman a fannin sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da kuma yadda kasashen duniya suka rungumi kasuwar kasar tare da baiwa hajojin kasar fifiko da karfin takararsu a kasuwannin duniya. 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping yayin ganawarsa da shugaban kasar Faransa a ranar Litinin a ziyararsa da ya kai Faransa, ya yi tsokaci kan wannan batu, inda ya ce, babu wani abu da ake kira “samar da kayyaki fiye da kima” idan aka yi la’akari da manufar gasar cinikayya, ko bukatar kasuwannin duniya. Biyo bayan damuwar kasashen yamma musamman game da karuwar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, kamar kayayyakin makamashin hasken, da motocin sabbin makamashi da batura. (Sanusi Chen, Mohammed Yahaya, Saminu Alhassan)