logo

HAUSA

Za a samu kyautatuwar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Faransa

2024-05-08 00:10:18 CMG Hausa

A ranar 6 ga wata, bisa agogon Faransa, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron sun yi ganawa a birnin Paris, inda suka cimma dimbin sakamako. A cewar shugaba Macron, duniya na fuskantar tarin manyan kalubaloli, saboda haka Fransa da kungiyar kasashen Turai ta EU suna bukatar karfafa hadin kai da kasar Sin, fiye da duk wani lokaci na baya.

A bana aka cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Faransa. Kuma a wannan lokaci na musamman, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya zabi Faransa a matsayin wuri na farko da ya ziyarta a  wannan shekarar da muke ciki. Hakan ya nuna yadda bangaren kasar Sin ke dora matukar muhimmanci kan huldarsa da kasar Faransa. Yayin da a nata bangare, kasar Faransa ta shirya dimbin bukukuwa don tarbar shugaba Xi na kasar Sin, da nishadantar da shi. Wadannan shirye shirye  da aka yi su ma sun nuna niyyar kasar Faransa ta zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin.

Sai dai ta yaya za a iya kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2? A cewar shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya kamata bangarorin 2 su dogara da kansu, da neman fahimtar juna, da nuna hagen nesa, gami da hadin gwiwa a kokarin haifar wa junansu alfanu. Kana kamata ya yi, a magance abkuwar yakin cacar baki, da arangama tsakanin rukunai daban daban. Wadannan shawarwari sun nuna alkiblar da Sin da Faransa za su dosa, a kokarin kyautata huldar dake tsakaninsu. (Bello Wang)