logo

HAUSA

Shugaba Xi Ya Sanar Da Matakai 6 Da Za Su Tallafa Wajen Gina Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya Ga Sin Da Serbia

2024-05-08 20:40:27 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanar da wasu matakai 6 da za su tallafawa gina al’ummar Sin da Serbia mai makoma ta bai daya.

Na farko, bisa hadin gwiwar Sin da Serbia, yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci tsakanin kasashen biyu za ta fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli.

Na biyu, kasar Sin tana goyon bayan Serbia ta karbi bakuncin bikin baje koli na duniya na shekarar 2027, kuma za ta tura tawagar da za ta halarci bikin.

Na uku, a shirye kasar Sin take ta karbi kayayyaki masu inganci da ma amfanin gona daga Serbia.

Na hudu, cikin shekaru 3 masu zuwa, bangaren Sin zai taimakawa matasa 50 masana kimiyya daga Serbia a shirye-shiryen musaya na kasar.

Na biyar, har ila yau cikin shekaru 3 masu zuwa, za a gayyaci jimilar matasan Serbia 300 domin su yi karatu a kasar Sin.

Na shida, kasar Sin na maraba da Serbia ta kara yawan zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin Belgrade da Shanghai, tare da karfafawa kamfanonin jiragen saman kasashen biyu gwiwar kaddamar da zirga-zirga kai tsaye tsakanin biranen Belgrade da Guangzhou.

Shugaba Xi Jinping ya sanar da wadannan matakai ne yayin da suke hira da manema labarai tare da shugaban Serbia Aleksandar Vučić. (Fa’iza Mustapha)