logo

HAUSA

Peng Liyuan da Brigitte Macron sun ziyarci gidan adana kayan tarihi na Orsay

2024-05-07 10:38:45 CMG Hausa

Da yammacin jiya Litinin, bisa gayyatar da aka yi mata, mai dakin shugaban kasar Sin Peng Liyuan, tare da mai dakin shugaban kasar Faransa Brigitte Macron, sun ziyarci gidan adana kayan tarihi na Orsay.

Yayin da suke kewayawa a sassan gidan, sun rika tsayawa jefi-jefi, domin yaba ayyuka masu kayatarwa na shahararrun masu zane-zane irin su Claude Monet, da Van Gogh, da Pierre-Auguste Renoir da sauran fitattu, inda suka rika musayar ra’ayoyi kan ayyukan.

Yayin da take tsokaci game da yadda al’ummun Sin da na Faransa ke matukar son zane-zane, uwargida Peng ta bayyana burinta na ganin al’ummun sassan biyu sun fadada musaya, ta yadda za a kara nishadantuwa daga al’adun juna, da zurfafa fahimtar juna. Peng ta kuma yi fatan cewa, masu fasahohin kasashen biyu za su karfafa musaya, da koyo daga juna, domin zaburar da juna wajen samar da karin ayyuka masu kayatarwa.

A zauren gidan na adana kayan tarihi, matan shugabannin kasashen biyu, sun gai da daliban kasar Faransa masu ziyara da nazari. (Saminu Alhassan)