logo

HAUSA

Hutun farkon watan Mayu ya nuna ci gaban tattalin arzikin Sin

2024-05-07 16:26:59 CMG Hausa

Bayanin da gwamnatin kasar Sin ta fidda ya nuna cewa, a yayin hutun murnar ranar ‘yan kwadago ta kasa da kasa na kwanaki 5 da aka yi a farkon watan Mayun nan, mutane miliyan 295 sun yi tafiye tafiyen yawon shakatawa a cikin kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 7.6 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kuma yawan kudin da suka kashe ya kai Yuan biliyan 166 da miliyan 890, adadin da ya karu da kaso 12.7%.

A sa’i daya kuma, akwai mutane da dama da suka tafi yawon shakatawa a kasashen duniya. Bayanin da aka samu ya nuna cewa, a lokacin hutun farkon watan Mayu, Sinawa sun yi yawon shakatawa a wuraren kasa da kasa sama da dubu 1, lamarin da ya ba da gudummawa ga farfado da tattalin arzikin sassan kasashen duniya.

Yadda harkokin tattalin arziki suka gudana a lokacin hutun, ya kasance muhimmiyar hanyar binciken yanayin tattalin arzikin kasar Sin. Yawan kudin da jama’a suka kashe kan harkokin yawon shakatawa ya zarce hasashen da aka yi, lamarin da ya nuna karfin tattalin arzikin kasar Sin.

Kwanan baya, hukumomin kasashen duniya sun daidaita hasashen da suka yi kan karuwar tattalin arzikin kasar Sin. Bayanin da kafar yada labarai ta Bloomberg News ta kasar Amurka ta fidda, ya nuna cewa, tsakanin shekarar 2024 zuwa shekarar 2029, aikace-aikacen tattalin arzikin kasar Sin zai kai kaso 21 bisa dari, cikin sabbin aikace-aikacin tattalin arzikin kasashen duniya. Wadannan bayanai da aka samu sun fallasa karyar da wasu mutanen yammacin kasashen duniya suka yi, cewar wai tattalin arzikin kasar Sin ya riga ya kai kolinsa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)