logo

HAUSA

Xi ya yi tattaunawa da Macron

2024-05-07 00:32:31 CGTN

A ranar 6 ga wannan wata da yamma, agogon kasar Faransa, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron sun yi tattaunawa a fadar Elysee.

Yayin tattaunawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya yi farin ciki matuka da kai ziyarar aiki karo na uku a kasar Faransa bisa gayyata, a lokacin da ake murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Faransa. Kuma yana fatan ziyararsa za ta bude sabon babin huldar dake tsakanin kasashen biyu, tare kuma da taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiyar duniya da ci gaban bil Adama.

Xi ya kara da cewa, a halin yanzu duniyarmu na fuskantar manyan sauye-sauye, ya dace kasashen Sin da Faransa su nace kan manufar dogara da kansu domin dakile “sabon yakin cacar baka” ko “nuna adawa tsakanin rukunoni”. Haka kuma su kara karfafa fahimtar juna domin ingiza zaman jituwa tsakanin kasa da kasa. Ban da haka, akwai bukata a yi hangen nesa, domin sa kaimi ga ci gaban duniya. A karshe dai, ya kamata su yi kokari domin samun ci gaba tare. (Jamila)