Xi ya halarci liyafar maraba da shugaban Faransa ya shirya
2024-05-07 05:03:01 CGTN
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci liyafar maraba da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya shirya a ranar 6 ga watan Mayu a agogon Faransa, inda ya gabatar da jawabi. A cikin jawabinsa, Xi ya bayyana cewa, Sin da Faransa abokai ne na musamman, kuma dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa dangantaka ce ta musamman tsakanin manyan kasashen duniya. Ta kasance ta musamman saboda kasashen biyu suna riko da ruhin 'yancin kai. Xi ya ce, bana shekara ce ta cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Faransa. Shekaru 60 sun shude, duk da sauye-sauyen da ake samu a yanayin kasa da kasa, shugabannin kasashen Sin da Faransa na zamanin da suka gabata sun nazarci da kuma tafiyar da wannan dangantaka da dabarun hangen nesa kuma na dogon lokaci.
Dangantakar Sin da Faransa ta musamman ce ta yadda suke fahimtar juna, a cewar Xi, ya kara da cewa, an kebe wannan shekarar a matsayin shekarar al'adu da yawon bude ido ta Sin da Faransa. Kasashen biyu za su iya amfani da shi a matsayin wata dama na kara fahimtar al'adun juna.
Xi ya kuma ci gaba da cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Faransa na da muhimmanci, domin dukkansu na sauke nauyin dake wuyansu. Duniyarmu a yau tana fuskantar sauye-sauye da tashin hankali. Kasancewarsu mambobi na dindindin na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, Sin da Faransa suna da alhakin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. Kasar Sin da Faransa sun amince da kara zurfafa amincewa da hadin gwiwa a tsakaninsu, da karfafa tuntubar juna da yin hadin gwiwa kan manyan batutuwan kasa da kasa, tare da ingiza fata a duniya mai cike da rudani da gano hanyar samun ci gaban bil'Adama. (Yahaya)